May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gabanin Kotu ta fara zaman yanke hukunci Yan Sanda sun fara korar Yan jarida daga Kotu

1 min read

Tawagar Yan Jaridu da suke harabar kutun sauraren kararrakin zaben Gwmanan Kano sun fuskanci cin zarafi daga wani jami’in Dan sanda

Wani Dan jarida da ke harabar kotun, ya bayyana mana cewa cikin wanda Yan sandan suka ciwa zarafi har da wakilin BBC da na Jaridar Daily Trust.

A wannan Larabar ne dai kotun sauraren kararrakin zaben Gwmanan Kano zata yanke hukunci kan korafin da APC keyi na kalubalantar nasarar Abba Kabiru Yusuf a matsayin Gwamnan Kano da Hukumar zabe ta kasa INEC ta ayyana wanda lashe zaben da akayi na wannan shekarar.

Sai dai yanzu haka muna dakon jin matsayar rundunar Yan san dan Kano kan wannan zargi da ake yiwa jami’in na dan Sanda da aikata wannan laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *