June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Alƙalan da suka yi shari’ata sun yi kuskure – Abba Kabir Yusuf

3 min read

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce alƙalan kotun da ta gudanar da shari’ar zaɓen gwamnan jihar sun yi kuskure a hukuncin da suka yi na soke zaɓensa.

A ranar Laraba 20 ga watan nan na Satumba ne kotun wadda ta saurari ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar da hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bai wa Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris na 2023 ta soke nasarar.

Kotun wadda ta gabatar da hukuncinta ta manhajar Zoom ta ce tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne ya ci zaɓen.

Ta ce ta soke ƙuri’a 165,633 da ta ce aringizo ne aka yi wa ɗan takarar jam’iyyar NNPP, wanda tun farko hukumar zaɓe ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

A ranar 29 ga watan Mayu, na 2023 ne aka rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Sai dai a wani taron manema labarai da gwamnan na Kano ya yi a ranar Laraba da daddare ya ce, ba su amince da hukuncin ba domin yana cike da kurakurai kamar yadda lauyoyinsu suka shaida musu.

Injiniya Abba Kabir ya ce ko kaɗan hukuncin ba zai rage musu ƙwarin gwiwa ko ya sanyaya musu gwiwa ba a kan yadda suke gudanar da ayyuka ga al’ummar jihar ta Kano ba.

Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa suna fatan kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriyar za ta gyara kura-kuran da ya ce wannan kotun ta farko ta yi wajen soke nasarar tasa.

Gwamnan ya bai wa al’ummar da suka zaɓe shi tabbacin cewa kotun ɗaukaka ƙara wadda suke da damar garzayawa gare ta a nan gaba za ta tabbatar masa ikon da jama’a suka ba shi na mulkinsu.

Ya jaddada cewa hukuncin ba zai sa su ja da baya ba za su tsaya tsayin daka bakin ƙarfinsu domin ganin nasarar da suka samu a zaɓen ta tabbata a wannan lokaci.

Gwamman ya kuma lashi takobin cewa idan har ita ma kotun ɗaukaka ƙara ba ta yi musu hukuncin da ya gamsar da su ba, za su yi amfani da damar da suke da ita wajen garzayawa har zuwa kotun ƙoli.

A yayin jawabin da ya gabatar ya kuma roƙi al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba.

Ita dai kotun da ta yi hukuncin wadda ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf ne bayan ta shafe wajen wata shida na sauraren bahasin kowane ɓangare a shari’ar.

Bayan sanar da matsayar kotun sauraron korafin zaben gwamnan a ranar Laraba, hukumomin jihar sun kakaba dokar hana fita domin gudun kauce wa tashin hankali.

Ko a lokacin da Hukumar zaben Najeriya ta sanar da nasarar Abba Kabir a zaben da ya gudana a watan Maris, an samu asarar dukiya a birnin na Kano, sanadiyyar murna daga wasu magoya baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *