An janye dokar haramta zirga-zirga a Kano
1 min read
A wani sako da mai magana da yawun rundunar yan sanda na Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa ta manhajar Whatapp yace an janye dokar.
A jiya ne dai gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan yan sanda CP Muhammed Usaini Gumel, ta sanar da sanya dokar, bayan da kotun sauraran kararrakin zabe ta ayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano na 2023.