December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba ma fargabar zuwa kotun ɗaukaka ƙara – Ganduje

1 min read

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya yaba da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano da ta tabbatar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Hon. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce hukuncin bai zo masa da mamaki ba, “saboda abubuwa guda biyu, na farko shi ne sanin abubuwan da suka faru a lokacin zaɓe, na biyu kuma al’umma sun riƙa gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah ya tabbatar mana da wanna nasara”.

Ganduje ya ce jam’iyyar APC ba ta da wata fargaba game da ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar NNPP mai mulki za ta ɗaukaka.

Shugaban APCn ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’in fatan alkairi da suke yi wa jam’iyyarsa a tsawon lokacin da aka ɗauka ana shari’ar.

A ranar Laraba ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna ta sanar da soke nasarar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *