Gamnan jihar Kano Injiniya Alhaji Abba Kabir Yusuf,ya cika alkawarin daya dauka na tura yarinya Nana kasar India domin ayi mata aikin Ido
1 min read
Nana ita da mahaifanta sun ziyarci mai girma gwamna a yau a gidan Gwamnatin jihar Kano inda gwamnan yayi musu rakiya zuwa mota domin tafiya kasar India.
Idan za’a iya tunawa Nana itace yarinyar data ringa kuka a shekarar 2019 kan tana bukar ganin Abba Gida Gida.
Bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan kano, Abba Kabir ya ziyarci Gidan su Nana domin dubata dakuma gaishe da iyayan ta wanda a wannan lokacin ya fahimci yarinyar tana fama da matsala Ido anan take ya dau alkawarin daukar nauyin ta zuwa kasar waje domin duba lafiyar idon nata wanda kuma a yau 21 /9/2023 ya cika wannan alkawarin.