December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu Garkuwa da Mutane sun kashe shahararren Dan Jarida – Bayan neman kudin fansa

1 min read

Ƙungiyar yan jaridu na ƙasa reshen jihar Zamfara, ta tabbatar da mutuwar Alhaji Hamisu Danjibga, wakilin kafar yaɗa labarai ta muryar Nigeria a jihar (VON).

Sakataren ƙungiyar na jihar, Ibrahim Ahmad, ne ya bayyana haka ranar Laraba a Gusau dake jihar ta Zamfara, inda yace wadanda suka kashe shi, sun jefar da gawarsa a ma’ajiyar bahaya (Soakaway), bayan kwanaki uku da ɓacewarsa.

Sai dai yace tuni jami’an yan sanda suka cafke wani mutum guda da ake zargin yana cikin wadanda suka kashe dan jaridar, bayan sun bukaci kuɗin fansa na Naira Miliyan Guda daga iyalinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *