June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

BREAKING NEWS – Wike ya soke mallakar filayen Peter Obi da na su Udo Udoma a Abuja

1 min read

Ministan Abuja Nyesom Wike ya soke ikon mallakar filayen ɗan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da na tsohon gwamnan Cross River Liyel Imoke da ke birnin tarayyar.

Cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar Abuja, Olusade Adesola ya fitar, ta nuna cewa filayen Peter Obi da na Imoke na daga cikin fuloti 165 da hukumomin babban birnin suka ƙwace.

Sanarwar ta ce Wike ya soke ikon mallakar filayen ne saboda rashin gina su da aka yi.

Sauran manyan mutanen da matakin soke mallakar filayen ya shafa, akwai tsohon ministan tsare-tsare na ƙasa, Udo Udoma da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Ufot Ekaett, da tsohon sanatan Edo ta Arewa, Sanata Victor Oyofo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *