May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ko Yaya ake ciki game da ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da bindiga suka sace

3 min read

Bayanai daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, tare da sace ɗalibai waɗanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Lamarin dai ya faru ne da asubahin ranar Juma’a, inda rahotanni ke cewa maharan sun kutsa gidajen kwanan ɗalibai guda uku a unguwar Sabon Gida da ke maƙwaftaka da jami’ar.

Bayanan na cewa ƴan bindigar sun samu nasarar kwashe kusan dukkanin ɗaliban da ke zaune a gidajen waɗanda ke daura da jami’ar.

Har yanzu dai hukumomi ba su yi ƙarin bayani kan lamarin ba.

Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi jigata daga ayyukan ƴan bindiga masu fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ko a cikin watan Fabarairun 2021, ƴan bindiga sun shiga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a jihar, inda suka sace ɗalibai mata 317.

Haka nan ma a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.

Maharan sun abka ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako da rana tsaka, inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkiɗa tare da jikkata karin wasu.

Ita dai gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal, ta ce tana ɗaukar duk matakan da suka dace wajen shawo kan lamarin, sai dai ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba.

A baya dai gwamnatocin da suka gabata a jihar sun ɗauki matakai daban-daban, ciki har da na yarjejeniya da ƴan bindigar, sai dai har yanzu matsalar ta ci tura.

Ɗalibai da malamai sun ƙaurace
Waɗansu da BBC ta tattauna da su, waɗanda suka samu shiga harabar jami’ar da ke Gusau, sun ce abubuwa sun tsaya cak.

“Gaba ɗaya za a iya cewa duk wanda ke cikin jami’ar sun taru wuri ɗaya, babu wanda ke son ya je wani wuri, kuma ma babu mutane sosai, mutane kaɗan ne.” In ji ɗaya daga cikin waɗanda BBC ta zanta da su.

Ya ce da alama labarin harin ƴan bindigar ne ya sanya da dama daga cikin ɗalibai da kuma malamai suka ƙi shiga jami’ar da safiyar ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa ko a lokacin da ya shiga ginin ofososhin gudanarwa na jami’ar, yawancin su suna a kulle, kuma babu hada-hada ko gilmawar mutane kamar yadda aka saba.

Bugu da ƙari, an soke wasu daga cikin darussan da suka kamata a ce sun gudana da safiyar juma’a.

“Muna da lectures da safe, amma duk ba a yi ba.” In ji ɗaya daga cikin waɗanda suka tattauna da BBC.

Jami’an tsaro
Duk da dai babu tsattsauran matakan tsaro da aka ɗauka, amma da alamun akwai ƙarin jami’an tsaro da ke sintiri a kusa da jami’ar.

Waɗanda suka samu shiga harabar, sun bayyana cewa sai da jami’an tsaro suka tantance kafin a basu izini, kasancewar akwai jami’an tsaro da suka yi tunga a bakin ƙofar shiga jami’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *