Kotun ƙarshe ta tabbatar da Sanata Hanga na NNPP a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya
1 min read
Kotun ta kori ƙarar da AA Zaura na APC ya shigar a kotun ɗaukaka Kara.
Barrister Muhamand Nasiru Musa ɗaya daga cikin Lauyoyin da ke kare Sanata Hanga a Kotu ya tabbatarwa da Premier Radio cewa a yanzu Sanata Hanga na NNPP zai ci gaba da zama Sanata har karshen wa’adin majalisa ta 10.
A bisa tsarin doka kotun ɗaukaka ƙara, ita ce dama ta karshe ga wanda bai samu nasara a gaban kuliya ba, abinda ke alamta Itace kotun Allah ya isa a kujerar majalisar dattawa.