May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan sanda sun ce sun kama waɗanda ake zargi da yin garkuwa d amutane guda 20 a jihar Taraba

1 min read

Hakan ya biyo tattara bayanan sirri da samun korafe-korafe wajen jama’a kan munanan ayyukan masu garkuwan, da suka addabi sassan jihar.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Jalingo, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Usman, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin duk sun amsa aikata laifi.

Ya ce jami’ansu suka ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da kuma wata karamar bindiga kirar famfo.

A cewarsa, mutanen da ake zargin sun karɓi sama da naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa daga iyalan waɗanda suka sace wa ƴan uwa.

“Rundunar ‘yan sandan ba ta ja da baya ba a ƙoƙarinta na ci gaba da farautar ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun,” in ji shi.

Usman ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar ‘yan ta’adda a wasu wuraren da suka fi zafafa ayyukansu, musamman ma a Jalingo, babban birnin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *