May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kano ta sanar da sababbin motocin Asbiti ga kananan Hukumomin 44

1 min read

Cikin Yardar Allah tuni Mai Girma Gwamna H.E Alhaji Abba Kabir Yusuf yabada umarnin samar da motocin Asibitin tafi da Gidanka (Ambulance) wayanda za,a raba a kananan Hukumomin kano 44 dake fadin jihar Kano.

Idan baza amanta ba a lokacinda Mai Girma Gwamna Alhaji Abba kabir Yusuf yake Gangamin Yakin neman zabe yayi Alkawarin Siyan wayannan motoci domin bayar da guda 1, a kowacce karamar hukuma inda wannan mota yace za,a ajjeta a hedkwatar kowacce karamar hukuma yadda daga ansamu mara lafiya acikin lunguna da sako zasu sanar nan take wannan mota dake dauke da gado da magunguna zata shigo domin duba wannan mara lafiya idan kuma abin yaci tura adakko mara lafiyar zuwa babban asibtin wannan karamar hukuma dan nemasa lafiya.

Inda zuwa yanzu haka anfara kawo wayannan motoci kamar yadda Mai Girma Gwamna yabada Umarni.

Hon Salisu Muhammad Kosawa
SSA II On Social Media to the Executive Governor of Kano State H.E Abba Kabir Yusuf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *