May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai

1 min read

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai.

Sakataren hukumar bayar da tallafin ilimi ta jihar Kano, Hon. Kabir Getso Haruna ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

Yana mai cewa, “Yanzu haka Gwamnatin Kano, ta biya wa ɗalibai ƴan asalin jihar, dubu bakwai kuɗin makarantar”.

Inda ya Kara da cewa, dukkan ɗaliban, su tafi Jami’ar Bayero, tsangayoyin su, domin ƙarasa rijista don su ci gaba da karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *