May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rahotanni na nuni da cewa Nigeria ta Samu mummunar faduwar darajarar Naira a tarihi wanda ba’a taba Ganin irinsa ba

3 min read

Darajar kuɗin Najeriya ta yi wata mummunar faɗuwa da ba ta taba yin irinta ba, tun bayan ƙaddamar da naira a watan Janairun 1973.

A lokacin da naira ta maye gurbin tsohon kuɗin fam, da kasar ta yi amfani da shi. Hukumomi sun sanya darajar kuɗin, a kan naira ɗaya daidai da shilling ko sule goma.

Sai dai, shekara hamsin bayan samar da kuɗin, darajar naira na fuskantar jarrabawa da ba ta taba fuskanta ba a gomman shekarunta. Har ta kai a wani lokaci cikin wannan mako, an canji dalar Amurka ɗaya a kan takardar naira mafi girman daraja, wato naira dubu guda.

Ko da yake, farashin hukuma har yanzu ana sayar da dala daya a kan naira 785 ya zuwa yammacin ranar Talata.

Wasu masanan tattalin arziki na ganin karyewar darajar naira, wata barazana ce ga Najeriya.

Faɗuwar darajar naira a kasuwar canji, kamar yadda masu cinikin kuɗin suka bayyana, ta faru ne saboda buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje musamman dalar Amurka, wadda ta yi ƙaranci a cibiyoyin da ke hada-hadar kuɗin a farashin hukuma da kuma masu shaci-fadin farashi.

An sayar da dala ɗaya a kan sama da naira 1,000, kafin ta sauko zuwa naira 995 da safiyar Talata a kasuwar canji ta Abuja, in ji wani mai hada-hadar kudi. A makon da ya gabata, dala daya an sayar da ita a farashin naira 980.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani ɗan canji yana cewa mako uku kenan Babban Bankin kasar bai samar da dala a cibiyar hada-hadar kuɗin hukuma ba, abin da ya ta’azzara karyewar darajar naira.

Lamarin na faruwa ne daidai lokacin da sabon Babban Bankin Kasar Olayemi Cardoso ya kama aiki, bayan majalisa ta tabbatar da naɗa shi, kan wannan muhimmin mukami.

Wani mai canji a kasuwar canji dake bakin Wapa Kano, Alhaji Auwalu Soja, ya shaida wa BBC cewa, a Kano, ma an samu tashin farashin dala da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi.

“Muna iya bakin ƙoƙarinmu saboda ba gwamnati ce ke ba mu dalar ba, mu ne muke iya bakin ƙoƙarinmu wajen samo kudin don biya wa kwastomominmu buƙata.”

“A ranar Talata 26 ga watan Satumba, muna sayen dala a kan naira 980, mu sayar da ita naira 995, amma gaskiya a nan Kano, farashin dala bai taɓa kai wa 1,000 ba.

Amma mun sa mu labari a wasu sassan (kasar) cewa ta kai hakan,” in ji shi.

Ina matsalar take?
Gwamnati kullum na cewa tana ƙoƙari wajen ganin ta shawo kan matsalar, inda a baya babban bankin kasar ke samar da dala ga ƴan kasuwa a farashin hukuma.

Sai dai bayan hawan mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, sai gwamnati ta fitar da wani tsarin da ta kira “kasuwa ta yi halinta”.

Masana tattalin arziki a kasar na ganin ƙarfin arziƙin Najeriya, bai kai a saki kasuwar musayar kuɗi ba kaidi ba, saboda hakan na iya haddasa hauhauwar farashin dala, lamarin da ke faruwa yanzu haka kenan.

Dr Murtala Abdullahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziƙi a Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua Katsina, ya ce ” Lamarin akwai tashin hankali saboda idan dala ta kai naira dubu ɗaya, ko ba ta da taƙamaiman farashi, to zai shafi tattalin arziƙin Najeriya gaba ɗaya, saboda yadda ƙasar ta dogara da dala.”

A cewarsa, “Za a iya kwatanta tashin farashin dala a Najeriya da kamar mutum mai zazzaɓi, da ya fara da ciwon kai, kenan akwai yiwuwar komai zai iya ƙara taɓarɓarewa gaba kaɗan.

“Matukar kuma ba a yi hoɓɓasa ba, tattalin arzikin zai iya shiga mummunan yanayin da zai yi wahalar fita.”

Masanin ya ce tashin dalar na iya jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Ya ce babbar matsala ce idan ya kasance abin da ƙasa ke samu, bai kai abin da take kashewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *