May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya

1 min read

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 31 a cikin watanni 12 da suka gabata farawa daga watan Yulin 2022 zuwa Yulin 2023.

Cikin wani rahoto da NBS ɗin ta fitar kan ‘farashin kayan abinci’, ta ce jihohin Ebonyi da Abia ne aka fi samun hauhawar farashin.

A cewar rahoton, an fi samun tashin farashin ne a doya, wanda ya tashi da kashi 42, daga N389.75 a watan Yulin 2022 zuwa N539.41 a 2023.

NBS ta ce ba ya ga doya, sai kuma farashin shinkafa wanda ya tashi daga N467.80 zuwa N653.49 a cikin watanni 12.

Haka-zalika, farashin manja shi ma ya tashi da kashi 35 cikin 100, daga N890.67 zuwa N1208.62.

Sauran kayan abincin da farashinsu ya tashi sun haɗa da garin kwaki, wanda ya ƙaru da kashi 33 cikin 100, daga N323.17 zuwa N429.89, da kuma biredi wanda ya karu daga N486.27 zuwa N651.78.

Sauran sun haɗa da tumatir da Alkama da kuma nama.

Rahoton na NBS ya nuna cewa an fi samu tsadar kayan abinci a jihohin Kudu-maso-Gabas, musamman ma Abia da Ebonyi.

A ɗaya ɓangaren kuma, an samu mafi saukin farashin kayan abinci a jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Kogi, Neja, da kuma Benue.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *