May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta umarci Gwamnatin Kano ta biya diyyar Rushe Shagunan Filin idi

1 min read

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta biya hadaddiyar kungiyar amintattun masu shaguna a filin Idi zunzurutun kuɗin diyya har Naira Biliyan 30 saboda rushewa masu shagunansu ba bisa ka’ida ba.

Mai Shari’a Samuel Amobede ne ya yanke hukuncin a yau juma’a bayan kammala sauraron Shari’ar .

Justice watch ta rawaito mai shari’a Samuel Amobeda ya ce rushe shagunan masallacin idin da gwamnatin jihar Kano ta yi, bata yi shi akan ƙa’ida ba kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *