May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jirage sun yi luguden bam kan mutanen da ake zargi ‘yan Boko Haram ne a Najeriya Tucano

2 min read

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta yi luguden wuta a kan mayakan da ta ce suna samun mafaka a Tumbun, yankunan da ke kusa da Tafkin Chadi a cikin jihar Borno.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, rundunar sojojin saman kasar ta ce jiragenta sun harba bama-bamai inda suka lalata maboyar wadanda ta kira ”yan ta’adda’ kuma ta tarwatsa sansaninsu.

Ta ce jiragenta sun kai hare-haren ne daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Satumba, lokacin da aka tabbatar da ayyukan ‘yan ta’adda, masu barazana ga cibiyoyin sojoji da fararen hula da ke zaune a Tumbun Fulani da Tumbun Shitu, in ji sojin sama.

Sanarwar da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin sama Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar na cewa an ga mayaka suna dora jarkoki a cikin motocin a-kori-kura da ake girkawa bindigogi har guda biyu da aka boye a cikin tsirrai.

Bayan kai hare-haren ne, sojojin saman sun ce an kashe dumbin ‘yan ta’adda, sannan an lalata motocin.

Haka zalika, hare-haren da jiragen yaki suka kai a Tumbun Shitu bayan an gano maboyar bata-gari rufe a karkashin surkuki, inda kuma aka hangi motocin a-kori-kura uku da ake girka wa bindigogi suna shiga. Ta ce bayan an yi luguden wutar, rundunar ta yi bibiya inda ta tabbatar da hallaka ”yan ta’adda da dama da kuma lalata motocin a-kori-kura’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *