May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

DSS ta kama wata Yar TikTok kan barazanar kai harin kunar bakin wake kan shari’ar kano

1 min read

Hukumar tsaro ta farin kayata ta DSS, ta kama Fildausi Musa Ahamadu, mai shekaru 23, bayan ta yi barazanar kashe kanta tare da kashe duk wadanda ke da alhakin nasarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar gwamna a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.

Alfijir Labarai ta rawaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da kama Fildausi Musa Ahamadu

A cikin faifan bidiyo, an ji Fildausi tana cewa zata kai wa babban alkalin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna hari, inda ta yi gargadin cewa duk inda ta gan ta, ba za ta damu da rike ta da bomb

Hakazalika, Fildausi wanda ke sanye da jar hula, ta gargadi Nasiru Yusuf Gawuna dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da cewa, “kada ka kuskura ka bayyana inda kake, in ba haka ba, ba na damu da buga maka rigar bama-bamai .

Haka kuma na kai wa mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima hari, inda ta dora masa laifin dambarwar jam’iyyar NNPP a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *