May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar Kano ta fara Biyan Dalibai Mata Albashi N20,000

2 min read

Kano Ta Fara Biyan Dalibai Mata Albashin

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara biyan albashin N20,000 a duk wata ga dalibai mata 45,000 da ke ƙananan makarantu da nufin ba wa iyayensu ƙwarin gwiwar tura ’ya’yansu mata makaranta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar cewa gwamnatin jihar ta fara biyan daliban, kuma nan ba da jimawa ba za ta dawo da shirin ciyar da dalibai da kuma motocin ɗaukar daukar su kyauta.

Domin bunkasa karatun ’ya’ya mata da ba wa iyayensu kwarin gwiwar tura su makaranta, mun fara shirin gwaji na biyan N20,000 ga dalibai mata sama da 45,000 domin taimaka wa iliminsu.

“Za mu dawo da shirin ciyar da dalibai da kuma motocin daukar dalibai kyauta zuwa makaranta da kuma dawo da su,” in ji shi a jawabinsa na ranar cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yanci.

Ya ce gwamnatin Kano na gina sabbin makarantu a duk kananan hukumomi 44 da ke jihar na nufin ganin yaran da ke gararamba a titi sun koma aji.

Abba ya kuma jaddada shirin gwamnatin Kano na tura dalibai 1,001 da suka kammala digirin farko da daraja ta daya zuwa kasashen waje domin karo ilimi.

Wani rahoton ilimi (AHIP) ya bayyana damuwa cewa dalibai 300,000 ne suka kammala makarantar sakandare a Jihar Kano, daga cikin mliyan biyu.

Daraktar AHIP, Hajiya Mairo Bello Garko, ce ta bayyana wa wani taron tattaunawa kan hanyoyin magance kalubalen da ke hana yara mata zuwa makaranta, cewa ya zam wajibi a dauki matakan da za su ba yaran kwarin gwiwa.

“Duk da cewa an samu karuwar yara da suka koma aji a jihar, amma matsalar ita ce ta zuwa aji na gaba da kuma ta samun kammala sakandare.

“Bincike ya nuna yara miliyan biyu ne suka shiga makarantu a jihar, amma daga cikinsu 300,000 ne kawai suka kammala sakandare saboda matsalar jarabawar zuwa ajin karshe, rashin ingantattun kayan aiki da sauransu,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *