May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Isra’ila ta umarci Falasɗinawa su fice daga gidajensu

4 min read

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da mazauna yankuna bakwai na Zirin Gaza cewa su bar gidajensu tare da tafiya tsakiyar birane domin neman mafaka yayin da take ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin mayakan Hamas.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC yadda iyalai ke tururuwa suna barin gidajensu inda suke neman mafaka a makarantu mallakin Majalisar Dinkin Duniya.

Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin Hamas
Yadda hayaƙi ya turnuƙe samaniya a lokacin da wani harin sama na sojojin Isra’ila ya sauka kan wani dogon bene a yankin GazaASALIN HOTON,EPA
Bayanan hoto,
Yadda hayaƙi ya turnuƙe samaniya a lokacin da wani harin sama na sojojin Isra’ila ya sauka kan wani dogon bene a yankin Gaza

Dakarun sama na Isara’ila sun saki wani bidiyo da ke nuna yadda makamansu suka sauka kan gine-gine da ke Zirin Gaza, inda aka ce sansanoni ne na sojojin Hamas.

Ta kuma ce jiragen yaƙinta na ci gaba da kai hare-hare kan “muhimman wuraren tafiyar da ayyuka” na Hamas.

An kuma samu rahotannin fashe-fashe a kusa da dogon ginin Watan Tower, wani wuri mai cike da hada-hadar kasuwanci a Gaza.

Yadda ta kasance bayan wani harin da Isra’ila ta kai a yankin FalasɗinawaASALIN HOTON,EPA
Bayanan hoto,
Yadda ta kasance bayan wani harin da Isra’ila ta kai a yankin Falasɗinawa

Aƙalla mutum 250 ne aka ruwaito sun mutu, wasu 1,100 sun samu raunuka bayan ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ƙaddamar da hari mafi muni a shekarun baya-bayan nan kan Isra’ila.

Gwamman mayaƙa daga cikin Gaza sun kutsa yankunan Yahudawa a kudancin Isra’ila yayin da suke samun kariyar makaman da ƙungiyar ke cillawa ta sama.

Mayaƙan na Hamas yanzu haka suna garkuwa da sojoji da fararen hula ƴan kasar Isra’ila.

Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da miyagun hare-hare ta sama a kan yankin Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa 232 tare da raunata wasu 1,600, kamar yadda ma’aikatan lafiya suka bayyana.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila “na cikin yanayi na yaƙi” sannan ya sha alwashin cewa ƙungiyar Hamas, wadda ita ce ke mulkin yankin Gaza za “ta ɗanɗana kuɗarta.”

Rundunar sojin Isra’ila ta taso da dakarunta na ko-ta-kwana, kuma ana sa ran cewa za ta ƙaddamar da samame ta ƙasa.

‘Yaƙi mai tsawo da wahala’
Firaminsitan Isra’ila, Benjamin NetanyahuASALIN HOTON,EPA
Bayanan hoto,
Firaminsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu

Firaminsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya shaida wa al’ummar ƙasarsa cewa “za a shiga wani yaƙi mai wahala da za a daɗe ana yi.”

A wata tattaunawa da jagororin tsaro na gwamnatinsa, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce: “Burinmu na farko shi ne mu kawar da dakarun maƙiya da suka kutso cikin ƙasarmu sannan mu dawo da tsaro da lumana a yankunan da aka kai wa farmaki.”

“Burinmu na biyu a lokaci guda shi ne mu gallaza wa maƙiya a Zirin Gaza.”

“Buri na uku shi ne mu ƙara toshe sauran ƙofofi ta yadda babu wani daban da zai yi kuskuren tsoma kansa cikin wannan yaƙi.”

Wannan ne tashin hankali mafi muni cikin shekaru da aka samu, a wani ɓangare na rashin jituwar da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Wannan karo an ga yadda mayakan Faladinawa suka tsallaka shinge zuwa cikin Isra’ila da sanyin asubahi.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da suke cilla rokoki daga Gaza – inda wasu daga cikin rokokin suka kai har birane masu nisa irin su Tel Aviv da kuma Ƙudus.

Yadda mayaƙan Falasɗinawa suka kutsa ta kusa da Zirin Gaza
Bayanan hoto,
Yadda mayaƙan Falasɗinawa suka kutsa ta kusa da Zirin Gaza

Babu cikakken bayani kan yadda mayakan na Hamas suka iya kutsawa ta ɗaya daga cikin kan iyaka mafiya tsaro a doron kasa.

Isra’ila ta ce jiragenta na yaki sun kaddamar da hare-hare ta sama a sansanonin Hamas da ke Gaza, kuma sun samu nasarar samun sansanonin sojin Hamas 17.

Bama-baman da dakarun Isra’ila suka jefa sun lalata wani bene mai hawa 11 a tsakiyar birnin Gaza, wanda ke kunshe da gidajen rediyon kungiyar Hamas.

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce an kashe wata malamar jinya da kuma wani mai tuka motar asibiti sanadiyyar hare-haren na Isra’ila a kan wasu asibitoci biyu na yankin Gaza.

Wasu daga cikin rokokin da Hamas ta harba zuwa Isra‘ila sun samu faɗawa kan gidajen mutane da motoci ne bayan sun shallake shingen kariya daga hare-haren sama na Isra’ila.

Mazauna wasu daga cikin biranen Isra’ila da lamarin ya shafa sun ce sun daɗe ba su tsinci kansu cikin irin wannan hali ba.

An rufe zirga-zirga a hanyoyi da dama na birnin Tel Aviv yayin da garin ya zama fayau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *