May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba za mu gushe ba har sai mun shafe Hamas daga doron kasa – Netanyahu

2 min read

Dare na uku kenan a jere Isra’ila na ruwan bama-bamai kan Gaza, a matsayin ramuwa kan harin da ƙungiyar Hamas ta Palasɗinu ta kai mata ranar Asabar.

Da yake jawabi kafin ƙaddamar da luguden, Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce harin na jiragen sama somin-taɓi ne kuma a yanzu Isra’ila na yaƙi ne don kare kanta.

A wani jawabi da ya yi wa jama’ar ƙasar, Mr Netanyahu ya ce kawo yanzu rundunarsa ta kai hari kan matsugunnan Hamas fiye da dubu biyu a Gaza.

Ya sha alwashin cewa sai sun ruguza duk wani yanki da Hamas ke ciki.

Ya ce “Mummunan harin da Hamas ta kai kan Isra’ilawan da ba su ji ba basu gani ba, ba ƙaramin abin tashin hankali bane.

”Sun kashe iyalai a gidajen mu, sun hallaka ɗaruruwan matasa da suka taru domin wani biki, sun kuma yi garkuwa da mata da yara da kuma tsofaffi. Sun kai hari kan ƙananan yara kuma sun ƙona wasu da dama” in ji shi.

A halin da ake ciki kuma, mai magana da yawun ƙungiyar mayaƙan Hamas ya ce ƙungiyar za ta fara kashe mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza idan har Isra’ila ta ci gaba da harba bama-bamai kan gidajen farar hula a Gazar ba tare da gargaɗi ba.

Ministan harkokin wajen Isra’ila ya tabbatar da cewa Hamas ta yi garkuwa da mutane fiye da ɗari, kuma rundunar sojin ƙasar ta ce tana da cikakken bayanin waɗanda aka tsaren, harma ta fara sanar da iyalan su.

Tuni dai Shugabannin ƙasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Italiya suka yi Allah-wadai da harin da ƙungiyar Hamas ta kai Isra’ilan.

Ƙawayen Isra’ilan biyar sun ce suna nan daram kan goyon-baya da kuma tallafawa Isra’ila wajen kare kanta.

Ƙasashen dai sun ce sun amince da halascin ƙoƙarin Palaɗinawa na samun ƴancin kai, amma ko kusa ƙungiyar Hamas bata wakiltar wancan ƙoƙari.

A jawabin da ya yi wajen wani taron bauta a Arewacin birnin Landan, Firaiminitsan Birtaniya Rishi Sunak ya ce “Birtaniya ta na goyon bayan Isra’ila a yaƙin da take da ta’addanci a yau da gobe da kuma kowanne lokaci.

”Mun riga mun lura da kalaman da wasu ke furtawa da ke neman kawo rashin kwanciyar hankali a nan, Ina bayar da tabbaci ga al’ummar yahudawa mazauna Birtaniya, waɗanda ke shiga ruɗani saboda afka masu da ake yi a duk lokacin da ƙasarsu ke yaƙi, cewa hakan ba za ta faru ba a Birtaniya, ba dai a wannan ƙarnin ba.”

A nasa ɓangaren shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya buƙaci ɓangarorin biyu su rungumi sulhu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *