May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Nigeria sun kashe Yan bindiga Sama da 100 a yayin da suke kokarin farwa Al’umma

2 min read

Rundunar sojin Najeriya ta ce kashe yan bindiga fiye da 100 a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da ke Arewa Maso Yammacin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan babban hafsan sojin Najeriyar, Janar Christopher Musa ya umarci dakarun su bi ƴan bindigar har maɓoyar su don kawar da su.

Rahotanni sun ce sashin sojin sama na rundunar Operation Hadarin Daji ce ta yi wannan aiki, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa yan bindigar suna kan hanyar su ta kai hari a wani kauye.

Majiya daga rundunar sojin ta ce dakarun rundunar sun yi amfani da jirgin sama wajen kashe yan bindigar da ke tafiya cikin ayari da mashinan su, a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru.

Akwai kuma raunata wasu yan bindigar da dama a yayin arangamar da suka yi da sojojin Najeriyar.

Wannan na zuwa ne ƙasa da kwana guda bayan da babban hafsan sojin Najeriyar, Janar Christopher Musa ya umarci dakarun nasa su gaggauta kawar da ƴan bindigar da ke addabar al’ummar ƙasar, musamman a jihohin Arewa Maso Yamma.

A lokacin wata ziyara da ya kai wa dakarun rundunar sojin Najeriya da ke yaki da ƙungiyar Boko Haram ne Janar Christopher Musa ya umarci dakarun su daina jira sai yan bindigar da sauran masu dauke da makamai sun kawo masu hari kafin su dauki mataki, inda ya bayar da umarnin bin masu laifin har mafakar su domin kawar da su.

“Kada ku kwanta a sansaninku kuna jira su zo, ku tabbata kun zakulo makiya da ke addabar mutanen mu ku kashe su. Abin da ya fi dacewa shi ne ku same su har maboyar su, kuma ku kawar da su’’ inji Janar Musa.

A lokacin waccan ziyara dai babban hafsan sojin Najeriyar ya isar da sakon shugaban kasar, Bola Tinubu wanda ya ce yana sane da sadaukarwar da dakarun sojin ke yi wajen yaki da yan bindiga da sauran masu tayar da kayar baya, da kuma neman zaunar da kasar lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *