May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An ɗaura auren Zawarawa 1,800 a Kano kamar yadda Gwamnatin Kano ta yi alkawari

1 min read

Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sun halarci shaida daurin auren a babban Masallacin juma’a na fadar masarautar Kano, karkashin jagorancin babban kwamandan hukumar HISBAH na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Jagoran kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya fara aiwatar da wannan tsari a lokacin da yake kan Kujerar gwamnan Kano, ya halarci wajen tare da sauran manyan baki daga wasu sassan Nigeria.

An gudanar da daurin auren ne a dukkan ƙananan hukumomi 44 dake jihar, wanda dama tuni aka tura da kayan Daki da sauran abubuwan buƙata na hidimar aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *