May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An bai wa maniyyatan Najeriya wa’adin mako uku su biya miliyan 4.5 kuɗin ajiya

1 min read

Hukumar Alhazan Najeriya ta bai wa maniyyata aikin hajjin bana wa’adin makonni uku da su biya naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiyarsu.

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne kasancewar makonni uku ne kawai suka rage mata na kammala daidaitawa da masu tafiyar da lamuran aikin Hajji a Saudiyya.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa – hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama’a na hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce hukumomin saudiyya sun sanya ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala duk wata tattaunawa da masu kula da lamuran aikin hajji na ƙasar.

Kan haka ne hukumar ke buƙatar samun ƙiyasin maniyyatan aikin hajin bana domin samun damar ƙayyade farashin aikin hajjin banan.

Sanda Usara ta ce fara shirye-shiryen aikin hajin 2024 da wuri ya sa hukumar Alhazan ƙasar da na jihohin ƙayyade kudin ajiya na naira miliyan 4.5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *