May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban NAHCON ya kai ziyarar aiki ma’aikatar harakokin ƙasashen waje

2 min read

A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar Fatima Sanda Usara ta sanya wa hannu ta ce a ranar Alhamis 12th Oktoba, 2023 Alhaji Zikrullah Kunle Hassan shugaban hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ya gana da ministan harkokin ƙasashen waje Ambasada Yusuf Tuggar OON, domin menan tallafin hukumar akan harkokin difilomasiyya game da harkokin aikin Hajji da Umrah. shugabannin sun gana ne a shalkwatar ma’aikatar harkokin ƙasashen waje da ke birnin tarayya Abuja.

A yayin ganawar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya gabatar da NAHCON ga ministan, inda ya bukace shi da ya wakilci Najeriya a yayin da za a sanya hannu akan yarjejeniyar aikin Hajjin 2024 wadda a ke sa ran yi a cikin watan Janairu 2024. A cewa Zikrullah Kunle Hassan ya miƙa goron gayyatar ne da wuri domin bawa ministan isasshen lokacin don kammala da ayyukan da ke gabansa.

Da ya ke nasa jawabin Ambasada Yusuf Tuggar ya bawa hukumar NAHCON tabbacin samun haɗin kan ma’aikatar harkokin ƙasashen waje akan duk wani abu da zai ƙara kyautata walwalar alhazai da kuma ƙara daga martabar Najeriya. Sannan ya bayyana aniyarsa ta zuwa sanya hannu akan yarjejeniyar aikin Hajjin a cikin watan Janairun 2024.

A karshe ganawar dukkanin shugabannin sun amince da yin aiki tare, don haɓaka walwala da jindadin alhazai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *