May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Kano ya Bada umarnin tantance Malaman Makaranta dake tsarin Besda

1 min read

Yanzu yanzu: Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bada umarnin tantance Malaman Makaranta dake tsarin BESDA domin basu aiki na din-din-din ga wadanda suka cancanta.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin taron ƙaddamar rabon kayan karatu ga dalibai a Dakin taro na Coronation dake fadar Gidan gwamnatin Kano.

Yace ya bawa sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, tare da Kwamishinan ma’aikatar ilimi, Umar Haruna Doguwa, umarnin aiwatar da hakan, wanda za’a dauki mako biyu domin tantancewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *