May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sai na ga bayan ‘yan bindigar da suka addabi jihata — Gwamnan Katsina nan da Dan lokaci kadan

2 min read

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, Dikko Umaru Radda, ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo karshen matsalar ‘yan bindigar da suka addabi jiharsa.

Cikin wata hira da BBC, Gwamna Radda ya ce bangaren tsaro shi ne ya fi kowanne muhimmanci kuma tuni suka fahimci hakan shi ya sa ma aka yi doka don a kafa rundunar ‘yan sa-kai tare da ba su makamai da nufin taimaka wa jami’an tsaro.

Ya ce,” To yanzu mun kaddamar da su, mun horar da su mun ba su kayan aiki mun ba su motoci da babura da ma motoci masu sulke.”

Gwamnan na Katsina, ya ce dangane da batun biyansu kudaden alawus, gwamnatinsa ta dauki tsarin mafi karancin albashi wanda da shi ne za a rinka biyan ‘yan sa-kan alawus.

Dikko Radda, ya ce, “ Wani abu da ya kamata kuma mutane su sani, shi ne su wadannan ‘yan sa-kan su ne wadanda a garuruwansu suke irin wannan aiki ba tare da an biya su ko sisi ba, kuma suna wadannan ayyuka ne saboda su kare mutuncin iyayensu da ‘yan uwansu da kuma danginsu.”

Ya ce, “ Batun da wasu ke yi cewa irin wadannan ‘yan sintiri su ke kara dagula al’amura a harkar tsaro, zance ne na banza domin duk wanda ke zaune a wuraren da ke fama da matsalar tsaro ya san abin da ke faruwa, ta yaya za a kare mutanen da ke sace mutane su ci mutuncinsu da kashesu, ai ba abu ne mai wuya ba.”

Gwamnan na Katsina, ya ce,” Wallahi tallahi a matsayina na gwamna sai dai raina ya fita ba zan yarda wani ya zo ya ci mutane ba bayan ina da yadda zan yi, don wannan matsala ta kai halin da dole a hada kai domin ganin cewa an kawo karshen wannan matsalar don matsala ce da ta dame mu.”

Ya ce, “Duk wanda ke wani surutu akasin hakan saboda ba ‘yan uwansa ake kashe wa ba ne shi ya sa.”

Gwamna Radda ya ce, “ Kuma nan ba da jimawa ba idan an kammala duk shirye-shiryen da suka dace za a fara shiga daji da ni ma.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *