May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikici ya barke a zauran Malisar Dattijan Nigeria akan bude iyakar Nijar da Nigeria

2 min read

An samu rashin jituwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya da Mai tsawatarwa na majalisar yayin wani zama a yau Talata, lamarin da ya kai ga ficewar Sanata Ali Ndume daga zauren.

Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya bukaci majalisar ta shiga taron gaggawa na sirri bayan fitar mai tsawatarwa a kan wani hukunci da ya ce Ndume ya sauka daga kan ka’ida.

Sanata Ndume ya bijiro da wani kuduri ne a kan zargin tafka kura-kurai, ba kuma tare da an yi gyara ba daga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.

Kuskuren da Ndume ya yi jan hankali a kai na da alaka da wani kuduri da Sanata Kawu Sumaila ya gabatar don yin muhawara a kan bukatar a sake bude kan iyakar Najeriya da Nijar, ba tare da ya bayyana sunan kudurin nasa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mai tsawatarwa na majalisar dattijan wanda ya mike a zauren ya kafa hujja da oda ta 51 ta kundin dokokin gudanar da zaman majalisar dattijai, ya bukaci shugaban majalisar ya ba da dama a rika yin gyara kan duk wani kuskure da aka yi, ko kuma aka lura da shi a lokacin zaman majalisa.

Ndume ya ce, ”Wannan Majalisar Dattijai ce ta Jamhuriyar Tarayyar Najeriya da ke aiki bisa dokoki da ka’idoji da tsare-tsare. Idan a lokacin zaman majalisa, aka lura da yin kura-kurai, wajibi ne a yi gyara a kansu kafin a ci gaba da gudanar da muhawara.”

Sai dai cikin hanzari Sanata Akpabio ya katse shi, inda ya ce tun da an yanke hukunci a kan wadannan batutuwa da aka bijiro da su, ba za a iya sake waiwayarsu ba, don haka ya yanke hukuncin cewa Sanata Ndume ba ya kan ka’ida.

Sanata Sunday Karimi daga nan ya mike a zauren majalisa, inda ya yi kokarin jaddada bayanin Sanata Ali Ndume ta hanyar wani kuduri, amma sai Shugaban Majalisar Dattijai cikin sauri ya yanke hukuncin cewa shi ma ya sauka daga kan ka’ida.

Sai dai a wani yunkuri na kashe wutar dambarwa, Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, cikin hanzari ya mike inda ya karanta oda ta 16, wadda ta bukaci gabatar da wani kwakkwaran kuduri daga duk wani sanata don yin gyara ko bita a kan matakin da aka dauka tun da farko.

Cikin fushi, Sanata Ndume ya gabatar da wani kuduri da ke neman yin gyara a kan kuskuren da ake jin an aikata.

Amma ba tare da ya kammala gabatar da bahasi ba, sai Sanata Godswill Akpabio ya sake yanke hukuncin cewa Ndume ya sauka daga kan ka’ida. Lamarin dai a cewar Punch ya harzuka Ali Ndume, wanda ya tattara takardunsa, ya fice daga cikin zauren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *