May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zamanta na shirin yanke hukunci kan wasu sojoji biyu da aka gurfanar kan kashe Marigayi Sheikh Goni Aisami bayan kammala sauraren shari’ar kisan kai

1 min read

A watan Augustan shekarar 2022 aka kama sojojin kan halaka malamin ta hanyar bindige shi a hanyar Kano zuwa Gashua, inda aka kama su a cikin motarsa.

Wannan shari’ar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar Yobe da wadannan mutane biyu, Kofur John Gabriel da Adamu Gideon, ta tattara shaidu da dama da aka gabatar.

A ranar Laraba mai shigar da kara ga gwamnatin jihar, Barista A.S Mohammed, da kuma Barista D.M mai kare wadanda ake kara, suka yi muhawararsu ta karshe.

Kofur John Gabriel ya amsa a gaban Alkalin kotun cewa, shi ne ya kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin kamar yadda ake zargin sa da aikata.

Bayan alkalin kotun, Mai shari’a Usman Zanna Mohammed, ya saurari dukkan hujjoji da bayanan da bangarorin suka gabatar, ya dage zaman domin yanke hukunci na karshe wanda nan gaba za a sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *