May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Idan shekara 1000 za ayi, bazan saki mata ta ba, domin ina son ta har yanzu – G-Fresh

1 min read

Mawaƙi Abubakar Ibrahim (G-Fresh Al-amin, Kano State Material), yace ko shekara dubu za ayi nan gaba, bazai saki matarsa Sadiya Haruna ba, kuma har yanzu ana kan batun sulhu ne a Kotu.

Tun bayan samun saɓani tsakanin ma’auratan, aka gaza gane hakikanin abinda ya faru, domin ita Sadiya Haruna ta ce sun rabu da G-Fresh, amma kuma ya kafe akan cewa bai sake ta ba, kuma bazai sake ta ba.

Komai zai zo karshe ne idan lokacin da kotu ta kammala sauraro tare da yanke hukunci akan shari’ar yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *