May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Najeriya za ta gina rukunin gidaje 34,500 a faɗin ƙasar

2 min read

Ministan gidaje da raya birane, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na rukunin gidaje kusan 34,500 a faɗin ƙasa, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin bunƙasa al’ummomi masu ayyukan haɗin gwiwa a Najeriya.

Arc. Dangiwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce biranen da za a gina za su kasance cikin matakai, inda a mataki na farko, ake da niyyar ginda rukunin gidaje 34,500 a cikin jihohi talatin 30 na ƙasar.

Ya ce gidajen za su kuma kasance cikin rahusa domin mutane su samu damar mallaka.

Ministan ya ce don yin haka, ma’aikatar za ta yi da aiki da bankin bayar da rancen gina gidaje na Najeriya (FMBN) don bai wa masu cin gajiyar damar samun rancen gidajen a cikin rahusa, wanda za su iya biya cikin shekaru 30.

Ya kara da cewa “Muna shirin haɗa gwiwa da masu ci gaban kamfanoni masu zaman kansu don sayar da manyan gine-ginen a farashin kasuwa domin mu yi amfani da ribar da za a samu wajen rage farashin gidajen don masu karamin ƙarfi.”

Minista ya ce don cimma hakan, ma’aikatar za ta buƙaci goyon bayan gwamnonin jihohi wajen samun fili kyauta a matsayin gudunmawarsu ga shirye-shiryen gwamnati na gina gidaje masu sauki ga kowane ɓangare na al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *