May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tura ɗalibai karatu ƙasashen waje ƙarya ne da coge, kuma wallahi wasu jami’oin namu na Gida sunfi na ƙasashen wajen nagarta

1 min read


Kalaman tsohon gwamnan Kano kuma shugaban riƙon jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya furta a matsayin martani bayan tura Ɗalibai karatu zuwa ƙasashen ƙetare da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf tayi a baya bayan nan, domin su yi karatun Digiri na biyu.

Ganduje ya ce da yawa jami’oin cikin Gida sunfi wasu na ƙasashen wajen da ake gani nagarta, kuma a lissafin da su kayi, sun gano cewa, kuɗin da za’a kashewa yaro daya domin karatu a ƙasar waje, ya isa a kashewa yara 50 suyi karatu a Gida Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *