May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Syria ta ce Isra’ila ta kashe sojojinta takwas

1 min read

Sojojin Siriya 8 ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin soji a lardin Daraa da ke kudancin ƙasar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran Syria SANA ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 01:45 agogon kasar a ranar Laraba.

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da kai hari kan yankunan Siriya – inda ta ce jiragen yaƙinta sun kai hari kan kayayyakin aikin soji da na harba rokoki bayan da aka harba rokoki daga bakin iyakar ƙasar zuwa Isra’ila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *