May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Halin da ake ciki -Ƙungiyar Red Cross ta yi kiran a gagguta tsagaita wuta a Gaza

2 min read

Ƙungiyar bayar da agaji ta duniya, ICRC ta yi kiran a gagguta kawo ƙarshen yaƙin Gaza don kaucewa abin da ta kira mummunan asarar rayuka da kuma wahalar da mutane ke ciki a yankin.

Tun bayan harin da Hamas ta kai Isra’ila makwanni 3, ICRC ke ci gaba da kiran a saki mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma neman bayar da damar shiga Gaza don kai agajin gaggawa.

Ba dai kasafai ICRC ke fita ƙarara ta yi tsokaci game da yadda yaƙi ke gudana ba, amma tana jajircewa wajen ganin dukkan ɓangarorin da ke yaƙin sun mutumta dokar ƙasa da ƙasa.

Amma a ranar Lahadi ta fitar da gargaɗi mai tsaurin gaske, tana cewa akwai fararen hula miliyan biyu da suka maƙale a Gaza, waɗanda basu da wajen tserewa, ga kuma luguden wuta ana yi masu.

Sanarwar da Red Cross ta fitar ta yi gargadin cewa dole duniya ta nuna ƙyamar abin da ke faruwa don kaucewa mummunar annobar da ke tafe.

Ta yi Allah-wadai da yadda ake fakewa da fararen hula yayin yaƙin, sannan ta sake yin kiran a saki mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ta kuma jaddada cewa abin da ya fi damun ta a yanzu shi ne yadda za a bai wa ƙungiyoyin agaji, ciki harda jami’anta, damar shiga don kai tallafi Gaza ba tare da fuskantar hatsarin da suke gani a yanzu ba.

Tun da farko dai, sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya yi mamakin yadda Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza, sai dai ya ji daɗin yadda duniya ta haɗu wajen neman kawo ƙarshen yaƙin da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *