May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Gano mutane 104 da jirgin ruwa ya kife da su a Taraba

2 min read

Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto, don gano mutum kusan ɗari da har yanzu ake ci gaba da neman tun bayan nutsewar wani jirgin ruwa a jihar Taraba.

Tuni dai aka yi jana’izar kusan mutum 17 da suka mutu, sanadin wannan al’amari a kan hanyarsu ta zuwa Mayo Raneyo daga Binnari a yankin ƙaramar hukumar Karim-Lamido.

Hukumar ta NEMA tace sama da mutum ɗari ne haɗarin jirgin ruwan ya rutsa dasu.

An dai shiga rana ta uku a aikin ceton da ake gudanarwa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce jirgin ruwan ya kife ne a lokacin da yake dauke da kimanin fasinjoji 100, akasari ‘yan kasuwa daga garin Mayo Raneyo da ke yankin ƙaramar hukumar Arɗo Kolo.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya shaida wa BBC cewa cikin wadanda hadarin ya rutsa da su har da mata da kananan yara

“Jirgin na ɗauke da kaya da mutane, wasu sun sayo kayan furobishin, wasu sun yi cefanan gari, wasu ma sun sayi sabbin mashina ne a cikin jirgin za su koma gida.

“A ranar Asabar an samu gawa guda, a ranar Lahadi kuma an sami gawa huɗu, an kuma ga wata gawa guda a wajen yunƙurin fito da ita ta sulluɓe ta koma cikin ruwa, kuma daga nan ba a san inda ta yi ba,” in ji ganau ɗin.

Ya nuna cewa an yi wa jirgin lodi mai yawa ne. Amma ga wanda ya san harkar jirgin ruwa ya san matuƙin ba shi da kwarewa sosai.

Kazalika wani mai aikin ceto ya ƙara shaida wa BBC cewa matsalar ɗaukar mutane da yawa da kullum ake kuka da ita, a yanzu ma ita ce ta kai ga kifewar jirgin.

“Tun kan a yi nisa aka gano nauyin jirgin ya fi ƙarfi a ɓangare guda, aka kuma yi wa matuƙin magana ya yi buris.

“A lokacin igiyar ruwa ta yi ƙarfi fiye da ake tsammani.

“Ya shiga tsakiyar ruwan ne injin jirgin ya tsaya suka maƙale, igiyar ruwa kuma da yake tana da ƙarfi ta kifar da jirgin,” in ji mai aikin ceton.

Dr Bashir Garga shi ne daraktan kula da ayyuakan ceto da gudanarwa a hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ya ce kawo yanzu sun ceto kusan mutum 12 da ransu.

“Jirgin yana ɗauke da aƙalla mutum 104, an cero gawar mutum 17, an kuma ceto 12 da ransu,” in ji Dr Garga.

Ya alaƙanta wannan haɗari da daukar fasinjoji fiye da kima, wata matsala da mahukunta kullum ke faman a kiyaye, suna cewa da muguwar rawa gwamma ƙin tashi. Da asarar rayuka haka da yawa gwara ba a yi tafiyar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *