May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu masu sukar gasar wakar Ƙidaya ta Rarara, Dusa ce ko Katako a Kan su – Aisha Humaira

2 min read

Jaruma a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, kuma abokiyar aikin mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara, wato Aisha Humaira, tayi kaca-kaca da wasu jaruman TikTok da suka soki gasar Waƙar Ƙidaya da Rarara ya rera, inda tace akwai wadanda Dusa ce ko Katako a Kan su, akwai kuma wadanda za’a yiwa uzuri domin basu fahimci abinda ake nufi da Ƙidaya ba.

Aisha Humaira wacce tayi martanin cikin wani fefen bidiyo, ta ce babu wanda aka yiwa dole akan gasar, kawai dai sun saka gasar ne domin kyautatawa ma’abota shafukan sada zumunta na zamani, domin su samu wani abu, amma kuma sai gashi anzo ana sukar abin, wanda dama halayyar yan Arewa ne, su soki duk wani abu mai kyau da dan uwansu ya fito dashi, a cewar ta.

“Rarara ba zai iya kawo karshen matsalar tsaro a Arewa ba, masu ganin kamar bai damu da matsalar tsaro ba, karku manta dan jihar Katsina ne, kullum cikin fargaba yake domin mahaifiyarsa da yan uwansa na can, kuma a baya yayi Waka akan matsalar tsaro, sannan kuma shi bai damu da zagin da kuke masa ba, mai ra’ayin shiga gasa ya shiga, mara ra’ayi kar ya shiga.”

Tunda fari dai wasu ma’abota shafukan sada zumunta ne suka soki batun gasar Waƙar Ƙidaya ta Rarara, bisa hujjar cewa bai yi Waƙar janyo hankalin mahukunta akan sha’anin tsaro ba, kuma bai shiga cikin kiraye-kirayen da aka yi akan kawo karshen matsalar tsaro musamman a Arewacin Nigeria ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *