May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani lokaci nakan koma gefe na fashe da kuka – Ɗan jarida daga Gaza

3 min read

Yana kira duk lokacin da ya samu dama. Ko kuma dai duk lokacin da ya samu damar yi wa wayarsa caji.

Yana cin abinci ne kawai idan ya samu. Yakan zagaya daga wurin da aka ɗaiɗaita zuwa wani matuƙar dai zai samu man fetur.

Bugu da ƙari, Mahmoud Bassamna cike da damuwa game da matarsa da ɗansa ɗan wata 11 saboda ya zama dole su yi hijira don guje wa hare-haren bam. Saboda duk lokacin da ya bar gida da safe ba shi da tabbas zai dawo ya tarar da su a inda ya bar su.

Ana maganar idan ma ya dawo ke nan. Ma’ana idan ba a tare hanyar ba ko kuma hare-haren sun yi ƙamarin da ba zai iya bin hanyar ba.

A Birnin Gaza a ‘yan kwanakin nan, rayuwar Mahmoud na cikin yaƙi, abin da zai haifar da kuma abin da asarar da yake haifarwa.

Tun bayan fara yaƙin nan sati uku da suka wuce, Mahmoud yake zagayawa asibitoci da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira.

Iriin wannan aikin nasa da kuma taimakon wakilin BBC Rushdi Abualouf, da su ne BBC take iya samun damar bayar da labaran fararen hular Gaza, waɗnda ke shan luuguden wutar Isra’ila a kodayushe.

Da na same shi ta waya bayan shafe awanni ina ƙoƙari, mahmoud ya bayyana irin wahalar aikin da yake yi.

“Duk irin ƙoƙarin da nake yi, da irin juriyar kallon abin da nake gani wajen nemo labarai,” in ji shi, “wani zubin sai na koma gefen kyamara na fashe da kuka. Daga baya kuma abin da zan yi shi ne shuru.”

‘Yan jaridar Gaza kan ɗauki labaran wahalar da ake sha wadda su ma suke cikinta ASALIN HOTON,EPA
Bayanan hoto,
‘Yan jaridar Gaza kan ɗauki labaran wahalar da ake sha wadda su ma suke cikinta

Akasarin ‘yan jaridar da na sani suna aiki a wuraren yaƙi kan ji cewa sun gaza saboda yawan wahalar da suke ganin mutane a ciki. Ta yaya za ka iya taimakawa bayan akwai masu buƙtar taimakon da yawa? Ta yaya za ka iya yin aikin idan ka tsaya taimaka wa mutane da abinci ko agaji?

Mu ba ma’aikatan agaji ba ne. Amma kuma mutane ne.

Irin wannan yanayi na ƙara zama tabbas a idanun Mahmoud idan ya haɗu da sauran abokansa. Wakilai da ke aiki da gidajen jarida na ƙasashen waje na da damar hawa jirgi su tanfi gida. Babu mamaki mu dinga yaƙin amma dai aƙalla mun yi nesa da shi da kuma iyalanmu.

Zirin Gaza ƙaramin wuri ne sosai – murabba’in kilomita 366 ne kawia baki ɗayan zirin. Mahmoud kan gano wani da ya sani a wannan wurin cikin sauƙi.

“Ni ɗan jarida ne kuma aikina shi ne bayar da rahoton abin da na gani,” kamar yadda ya faɗa min. “Amma wani zubin dole nake tsayawa mu zauna tare da yaran nan, don na ba su ruwa kuma na ga abin da suke buƙata don na ba su.”

Idan ya turo bidiyon da ya naɗa zuwa ofis, ni da sauran abokan aikina sai mu dinga mamakin irin natsuwarsa. Bai taɓa manatawa da cewa akasarin waɗanda yake ɗaukar hoto ko bidiyonsu ba su taɓa yin magana a kyamara ba a rayuwarsu a irin wannan halin.

Wannan yaƙin na ɗaya daga cikin waɗanda ‘yan jarida suka fi shan wahala. An kashe fiye da 30 zuwa yanzu. Cibiyar Committee to Protect Journalists (CPJ) ta ce waɗanda suke Gaza na ɗanɗana kuɗarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *