May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A yayin da Nigeria ke cigaba da kokawa game da tsadar rayuwa Shugaban kasa Tinubu na shirin kashe Naira Biliyan da rabi a Ofishin matar Shugaban kasa

2 min read

Yan Najeriya na ci gaba da nuna bacin rai da kwakwazo har a shafukan sada zumunta kan yunƙurin gwamnati na sayen sabbin motocin alfarma ga Uwargidan shugaban ƙasar, Remi Tinubu.

Suna kafa hujja da cewa halin da ƙasar ke ciki na ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziƙi, bai dace da kashe dukiyar al’umma wajen sayen motocin alfarma ga iyalin shugaban ƙasar ba.

A ranar Litinin ne, gwamnatin Najeriya ta amince da gabatar da wani ƙudurin kasafin kuɗi na cikon gibi da ya zarce naira tirliyan 2.17 ga majalisar dokokin Najeriya.

A cikin kudurin kasafin kuɗin, gwamnatin tarayya na da niyyar kashe naira biliyan 28 domin al’amuran gudanar da fadar shugaban kasa, inda za ta kashe sama da biliyan biyu wajen sayen motocin alfarma.

Sai kuma wata naira biliyan 2.9 da za a kashe wajen sayen motocin gudanar da ayyuka fadar.

Akwai kuma naira biliyan hudu na aikin gyare-graren gidan shugaban ƙasa, an kuma ware naira biliyan biyu da rabi na gyaran gidan mataimakinsa. Yayin da motocin da za a siya wa uwargidan shigaban ƙasa za su ci naira biliyan ɗaya da rabi.

Da shirin kashe naira biliyan 12.5 a bangaren jiragen saman fadar shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu ya sha kira ga ‘yan kasar su kara sadaukarwa a mawuyacin lokacin da kasar take ciki na matsin rayuwa, wanda janye tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi, ya kara tsunduma talakawa cikin wahala.

Ƴan Najeriya dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu musamman a shafukn sada zumunta, inda wasu da dama ke yin kakkausar suka a kan kashe makudan kudaden da suke gani ba zama lallai ba.

Mafi yawa dai na ganin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta tausaya wa halin da talakawan kasar ke ciki, matukar za ta kashe wadannan maƙudan kuɗaɗe a lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da yunwa da kuma bakin talauci.

Wannan batu ya yi daidai da ra’ayin wani mai suna Ibrahim a shafin X, wanda a baya aka fi sani da suna Tuwita.

…ASALIN HOTON,X
Shi ma wani mai amfani da shafin na X Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar ya yi gugar zana a kan batun sayen motocin alfarmar ga Remi Tinubu.

Ya dai wallafa wasu kalamai da ya yi ikirarin cewa Uwargidan shugaban ƙasar ce ta furta su a farkon hawansu mulkin Najeriya. Ga bayanin kamar haka:

“Ba a zabe mu don mu yi sata ba. Allah ya albarkaci rayuwar mijina. Ba ma bukatar dukiyar Najeriya don samun abin rayuwa. An zabe mu ne don kawo sauyi Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *