May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hisba ta kamo mutane 25 da ke aikata badala a wasu otel a kano

1 min read

A ci gaba da sumamen yaƙi da baɗala da Hukumar Hisbah ke yi a sassan Kano ta sake cafke maza da mata 25 a wannan dare na Alhamis.

Hisbah ta kai sumame Gidan Abinci na Juri da ke titin Asibitin Nassarawa, sai kuma Lasultana da ke titin Ahmadu Bello da kuma Banana da ke bayan filin Baje Koli.

Yayin sumamen Hisbah ta kamo mata 16 da maza 9.

Hisbah ta kuma koma kewaye inda ta kai sumame a jiya wato Piccolo sai dai ba ta samu waɗanda za ta kama ba, hakan ta sa yan Hisbah suka kaure da Kabbarori.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *