May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ma’aurata 1,800 sun maka tsohon kwamishinan Ganduje ƙara a gaban kotu

1 min read

Ma’auratan da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta yiwa auren gata, sun maka tsohon kwamishinan ma’aikatar harkokin Ruwa ta jihar Kano, Garba Yusuf Abubakar (Izala) ƙara a gaban kotun Addinin musulunci ta Shahuci, bisa zarginsa da bata musu aure a kafafen yaɗa labarai.

Isah Sadiku Muhammad da mutane 1,799 sun ce kalaman da Garba Izala ya furta sunyi musu ciwo, saboda haka ne suka garzayo gaban kotun Addinin musulunci domin a bi musu haƙƙinsu.

Alƙalin kotun mai Shari’a Abdullahi Abdu Wayya, ya sanya ranar 6 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki ta 2023 domin fara sauraron ƙarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *