May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Hisba da hukumar tace finafinai sun yi hadin gwiwa domin kauda badala a faɗin Jihar Kano

1 min read

Hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha da kuma hukumar Hisbah karkashin jagorancin Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa, sun shirya tsaf domin dakile yaduwar ayyukan badala a fadin jihar Kano.

Kakakin hukumar tace finafinai, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta, inda yace wannan ne dalilin da yasa Abba El-Mustapha yace dole kowanne dan masana’antar Kannywood ya sabunta rijista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *