May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria Aminu Maigari ya bayyana jindadinsa nisa karrama Bilal Nasidi Muazu na Freedom Radio Kano

1 min read

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria Aminu Maigari bayyana cewa karamawar da aka yiwa Bilal Nasidi Muazu a matsayin Best Sport Presenter a bude da ya kamata.


Alhaji Aminu ya bayyana haka ne a yayin bikin rufe gasar Alhaji Dr Ibrahim Galadima tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa ta Kasa Kuma tsohon Shugaban hukumar wasanni ta jihar.

Wasan Wanda ya gudana a Filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata, Kungiyar kwallon kafa ta Junior Kano Pillars ce ta kashe gasar bayan da ta doke Kungiyar Ahzuba daci daya da nema.

Alhaji Aminu Maigari ya ce Shima daya ne daga cikin mutanan dake sauraran shirin wasanni na Freedom Radio Kuma Bilal Nasidi Muazu nada daga cikin hazukan matasa Yan jarida da Kano tai alfahari da irin su.

Shima da yake jawabi Bilal Nasidi Muazu daga freedom Radio ya bayyana jindadinsa nisa wannan karramawa da aka Yi masa.

Ya Kuma ce wannan ya Kara masa kaimi wajen kara bunkasa bangaren wasanni a Kano da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *