May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A yayin da Al’ummar Nigeria ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa -Gwamnatin tarayya za ta gina gidaje dubu 30 kyauta ga ƴan ƙasa

1 min read

Gwannatin Najeriya ta ce tana shirin gina gidaje dubu biyar-biyar a dukkan shiyyoyi shida na kasar, don bunkasa samar da gidaje.

Ƙaramin ministan gidaje da raya karkara na Najeriya, Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da BBC dangane da bikin ranar inganta wuraren zama da gidaje na wannan shekara.

Ya ce dama akwai wannan tsari na gina gidaje a ƙasar, amma kasancewar wannan ma’aikatar a baya tana ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka da makamashi, amma yanzu an cire ta daga nan kuma za ta fara aiki gadan-gadan.

“Muna da shirin gina gidaje dubu dai-dai a kowacce jiha. Muna jiran Shugaban ƙasa ya sahhale mana ne sannan mu ƙaddamar da aikin, tsarin zai kasance waɗanda ba su da gata za’a basu kyauta, wasu kuma a ba su cikin farashi mai sauki,”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *