May 19, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Hisba ta Jihar Kano zata yiwa ƴan TikTok Auren Gata

1 min read

Babban kwamandan Hizbah na Kano Sheikh Aminu Daurawa ne ya faɗi haka, a taron tattaunawa da yiwa ƴan TikTok nasiha kan yadda zasu gyara tarbiyyar su.

Sheikh Daurawa yace dukkanin ƴan TikTok dake bukatar tallafi na jari, su rubutowa hukumar Hizbah irin sana’ar da zasuyi da kuma yadda zasu juya jarin, idan kuma aka gamsu da bayanan da suka bayar, gwamnatin Kano zata basu jari.

Yace Hizbah ta bullon da wannan salo bayan amincewar gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na taimakawa matasan da gyara musu tarbiyya.

Bayan kammala tattaunawar da ƴan TikTok manyan jami’an hukumar ta Hizbah sun haɗa kuɗi, Inda aka rabawa ƴan TikTok da suka halacci tattaunawar kuɗin mota Dubu bibbiyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *