May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Karota -Zamu Kori batagarin dake cikin domin inganta aikin

1 min read

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jiha KAROTA ta ce ya zama wajibi ta dauki matakin fitar da bata-garin cikinta domin inganta ayyukan Hukumar.

Shugaban Hukumar Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a wannan rana ta Alhamis lokacin da ya bayar da umarnin tsare wasu Jami’in KAROTA wadanda ake zargin su da matsawa direbobin mota da karbe-karben kudi a wajen su.

Yace Hukumar baza ta zuba ido ta bari a sauke tsarin da aka kafa Hukumar a kai ba, a don haka ya zama wajibi a hukunta duk wanda aka samu da sauya salon aikin Hukumar.

Ya ja hankalin direbobin mota da su guji bawa Jami’in hukumar ta KAROTA cin-hanci domin baya daga cikin manufar kafa Hukumar.

Ya kuma kara da cewa abinda ake bukata a wajen kowanne direba shi ne ya tabbatar ya mallaki dukkan takardun tuki kafin ya hau kan titi, da kuma bin dokokin hanya a lokacin da ake tokin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *