May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A kokarinta na kare Al’ummar jihar kano daga kamuwa da ko wacce irin cuta Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da allurar Sankarar mahaifa ga Yara Mata miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin

2 min read

Exif_JPEG_420

Gwamnatin jihar Kano ta ce,Yara mata daga Shekara 9 zuwa 14 su miliyan daya da dubu dari biyar da hamsin ne za’ayi wa allurar Sankarar mahaifa a jihar wanda aka Bude a yau Asabar a dakin taro na Asbitin Nasarawa dake nan kano.

Exif_JPEG_420

Kwamishinan Lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ne, ya bayyana haka, a yayin taron masu ruwa da tsaki na bangaren lafiya tare da kaddamar da Bude shirin a yau.

Kwamishinan ya kara da cewa allurar bata da wata illa ko hatsari wanda tuni ƙasashen duniya da dama sun dade suna gudanar da wannan allura domin kawar da cutar tare da kare lafiyar Yara mata kanana.

Exif_JPEG_420

Dr Abubakar ya kaddamar da gwajin allurar ga Yar sa domin zama shaida Al’umma wanda hakan ke tabbatarwa Al’ummar jihar Kano ingancin da Allurar dan kaucewa shakku ga iyayen Yara.

A cewar sa Gwamnatin tarayya ce ta sayo allurar, Kuma ta raba ga jihoyi goma shida domin farawa dasu,Kafin daga bisani ka kara fadada yawan aikin zuwa sauran jihoyi.

Za’a Kuma a dauki tsahon kwanaki biyar ana gudanar da Allurar,inda yayi kira ga Al’umma dasu fito da ‘Ya’Yansu mata domin yi musu riga kafin kyauata domin kare lafiyarsu.

Exif_JPEG_420

Taron dai ya Sami halartar jami’an Hukumomin lafiya daga sassa da dama da suka hadar da Hukumar lafiya ta duniya da unicef da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *