May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, ta dakatar da jarumin Kannywood Abdul Sahir (Malam Ali Kwana Casa’in), daga yin fim tsawon shekaru biyu

1 min read

Hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, ta dakatar da jarumin Kannywood Abdul Sahir (Malam Ali Kwana Casa’in), daga yin fim tsawon shekaru biyu.

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace sun ɗauki matakin ne saboda wani bidiyo da ya wallafa, wanda aka nemi ya kawo kansa zuwa hukumar amma yayi watsi da gayyatar har wa’adin da aka daukar masa ya cika.

Hukumar tace duk wani Darakta da yasan yayi fim tare dashi to ya gaggauta kawo fim dinsa zuwa hukumar domin a tantance shi, don gudun kada yayi asara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *