May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Kwadago ta NLC da Takwararta Ta TUC sun Umarci Dukkan Ma’aikatan Nigeria da su shiga Yajin Aikin sai Baba Ta Gani Daga 12 na Daren Wanann Rana ta Litinin

1 min read

Kungiyar Kwadago ta NLC da Takwararta Ta TUC sun Umarci Dukkan Ma’aikatan Nigeria da su shiga Yajin Aikin sai Baba Ta Gani Daga 12 na Daren Wanann Rana ta Litinin.

Kungiyar ta Cikin wata sanarwar Hadin Guiwa Da ta Fitar ta Bukaci Dukkan ma’aikatan Kasar Nan su kauracewa Wuraren Aikinsu Daga Gobe

Kungiyar ta Kuma umarci Dukkan Shugabaninta Dake Jihohin Kasar Nan su Tabbatar da ma’aikata sun bi Wannan Umarnin da ta Bayar har sai anji Sanarwa ta Gaba.

An Dade ana takun Saka tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnatin tarayya tun Bayan janye Tallafin manfetur da Gwamnatin Tayi

Acewar Kungiyar Gwamnatin tarayya ta Gaza cika Dukkan Alkawuran da ta dauka na saukakawa ma’aikata da sauran Yan Nigeria.

Haka Kuma abaya Bayan Nan Kungiyar ta Zargi jami’an tsaro da Gwamnan Jihar Imo Hope Udizunma da afkawa Shugaban Kungiyar Kwadago Ta Kasa Joe ajero wadda Ake zargin an raunashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *