May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dalilin soke bizar ‘yan Najeriya bayan isar su Saudiyya

2 min read

Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara bincike kan takamaiman dalilan da suka janyo soke bizar wasu gomman ‘yan kasar bayan sun sauka a Saudiyya ranar Lahadi.

Fasinjojin 264 waɗanda akasarinsu suka fito daga Legas da Abuja, sun isa filin jirgin sama na King Abdulaziz da ke Jidda a jirgin Air Peace, amma sai Saudiyya suka soke bizarsu, kuma nan take suka nemi a mayar da su gida.

Shugaban ƙungiyar kamfanoni da ke shirya aikin Hajji da Umara a Najeriya, Yahya Suleiman, ya faɗa wa BBC cewa mutanen sun je Saudiyya ne domin halartar taron kasuwanci tsakanin Saudiyya da ƙasashen Afirka, wanda aka gudanar a makon jiya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce tana so ta gano ko matsalar da aka samu ta shafi ofishin jakadanci ne, ko kuma wasu dokoki aka karya da suka shafi sufurin jiragen sama.

Ita ma ƙungiyar kamfanonin shirya aikin Hajji da Umara ta Najeriyar ta ce ta fara nata bincike kan lamarin.

Al’amarin ya faru ne jim kaɗan bayan Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da shugabanni da ‘yan kasuwar Saudiyya, har ma da na ƙasashen Larabawa yayin taron da aka yi tsakaninsu da ƙasashen Afirka.

Har yanzu, Najeriya ba ta warware rikicin hana wasu ‘yan ƙasar bizar shiga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ba, duk da sanarwar da gwamnatin Tinubu ta fitar cewa UAE ɗin ta ba da umarnin cire haramcin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *