May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida jikokinsa ‘Ya’Ya’ma’am na kenan) ya cigaba da kula dasu – Malam Ali

1 min read

Dakataccen jarumi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdul Sahir (Malam Ali), ya ce an dakatar dashi daga masana’antar ba bisa ƙa’ida ba, saboda haka ne yayi kira ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, akan cewa zai kawo masa jikokinsa domin ya cigaba da kula dasu.

Cikin wani fefen bidiyo da ya wallafa a ranar Talata, Malam Ali ya bayyana gwamnan Kano a matsayin Uba a gare shi, don haka yake so ya miƙa masa ‘ya’yansa kasancewar an dakatar dashi daga sana’ar da yake kula dasu.

A ranar Litinin ne hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta dakatar dashi tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da wallafa bidiyon da yake furta kalaman batsa, kuma ya ƙi amsa gayyatar da akayi masa domin kare kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *