May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

bindiga sun sace matar hakimi a Kaduna

1 min read

Wasu mahara da suka durfafi yankin yammacin ƙaramar hukumar Birnin Gwari sun shiga garin Kakangi inda suka sace mutum takwas, ciki har da matar tsohon hakimin garin.

Lamarin wanda ya faru a daren Laraba na zuwa ne bayan barazanar da ƴan fashin daji da ke addabar yankin suka umarci al’umma da su biya su miliyoyin kuɗaɗe dmoni tsira da hare-hare.

Ko a ranar Litinin, maharan sun far wa sojoji uku da aka ajiye domin tabbatar da tsaro a garin, inda suka harbi guda biyu daga cikin su yayin da ɗaya ya gudu a cikin mota mai sulke.

Yankin Birnin Gwari na daga cikin wuraren da suka yi ƙaurin suna kan matsalar ƴan fashin daji a Najeriya.

Hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, sai dai hare-haren na ci gaba da faruwa.

Wani mazaunin yankin ya ce a halin yanzu al’ummar yankin na rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas, kuma mutanen da dama sun kasa girbe ɗan amfanin gona da suka noma.

Akwai Karin bayani a nan gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *